Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi taƙaitacciyar ganawa da Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS, Mista Tosin Adeola Ajayi, a daren jiya Juma’a kan halin da ake ciki na tsaro a sassan ƙasar nan.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Ajayi ya gabatar wa da Shugaban Ƙasa cikakken bayani game da sababbin bayanan sirri da hukumar ta tattara kan matsalolin tsaro, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu jihohi da kuma matakan da jami’an tsaro suke ɗauka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ɗage tafiyar sa zuwa taron ƙoli na ƙasashen G20 da EU–AU da za a gudanar a Afrika ta Kuɗi da Angola, domin ya ci gaba da samun cikakken bayani da kuma jagorantar matakan gaggawa da ake ɗauka kan batutuwan tsaro, musamman lamarin sace ɗalibai a wasu yankuna.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu ya jaddada cewa babu wani aiki da ya fi muhimmanci ga gwamnatin sa kamar kare rayukan ’yan ƙasa, kuma saboda haka ya zauna a ƙasar domin ya tabbatar an ƙarfafa aikin haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro.
Shugaban ya kuma bada tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da dukkan ƙarfin ta wajen ganin an kawo ƙarshen hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa jama’a, tare da tabbatar da cewa ɗaliban da aka sace a jihohin Arewa-maso-yamma sun komo gida lafiya.
Hukumomin tsaro sun ce za su cigaba da aiki kafaɗa da kafaɗa domin tabbatar da tsaron rayuka, yayin da ake ƙara shigar da sababbin jami’ai da kayan aiki a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.







