• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya umurci Matawalle da ya koma Kebbi kan sace ɗalibai mata

ALI KANO by ALI KANO
November 21, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya umurci Matawalle da ya koma Kebbi kan sace ɗalibai mata
Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Muhammad Matawalle

Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Muhammad Matawalle

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Muhammad Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi ya zauna saboda sace ɗalibai mata 24 ɗin nan da aka yi a jihar.

Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar don sa ido kan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

Idan kun tuna, ’yan bindiga sun sace ɗalibai 24 na Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati (Government Girls Comprehensive Secondary School) da ke garin Maga, Jihar Kebbi, kimanin ƙarfe 4 na safe a ranar Litinin.

Ana sa ran Matawalle zai sauka a Birnin Kebbi a yau Juma’a, inda yake da ƙwarewa wajen tunkarar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane tun lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023.

A ranar 26 ga Fabrairu, 2021, ’yan fashi da makami sun sace ɗalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta ’Yan Mata ta Jangebe, wadda makarantar kwana ce a Jihar Zamfara. ’Yan fashin sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwa da su a ranar 2 ga Maris, 2021.

Tinubu dai ya ɗage tafiyar sa da aka tsara zuwa birnin Johannesburg a Afrika ta Kudu da Luanda a Angola, yana jiran ƙarin bayanan tsaro kan ɗaliban da aka sace a Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada na Cocin Christ Apostolic Church a Eruku, Jihar Kwara.

Tags: Bello Mohammed MatawalleKebbiMagasace ɗalibaiShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubuumurni
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin kan ƙasa da tsaron dijital — Minista

Next Post

’Yan ta’adda sun kai hari, sun sace ɗalibai da malamai daga Makarantar Katolika ta St Mary’s a Neja

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
’Yan ta’adda sun kai hari, sun sace ɗalibai da malamai daga Makarantar Katolika ta St Mary’s a Neja

’Yan ta’adda sun kai hari, sun sace ɗalibai da malamai daga Makarantar Katolika ta St Mary’s a Neja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!