• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Masu wulaƙanta naira ke ƙara haifar da tsadar buga sababbin kuɗi – CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 28, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Masu wulaƙanta naira ke ƙara haifar da tsadar buga sababbin kuɗi – CBN
Wani mutum ya duƙunƙune takardun naira yana ƙirgawa a wata kasuwa a Yola, Jihar Adamawa, a ranar 22 ga Fabrairu, 2023. (Hoto daga: REUTERS/Esa Alexander/Fayil)

Wani mutum ya duƙunƙune takardun naira yana ƙirgawa a wata kasuwa a Yola, Jihar Adamawa, a ranar 22 ga Fabrairu, 2023. (Hoto daga: REUTERS/Esa Alexander/Fayil)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce masu wulaƙanta takardun naira ne ke haddasa yawan hauhawar tsadar buga sababbin kuɗi a Nijeriya.

Wannan jan-kunnen ya fito ne daga bakin Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Sashen Ayyukan Yau da Kullum, Bala Bello, yayin da yake jawabi wurin rangadin wayar da kan jama’a dangane da yadda za a riƙa tu’ammali da takardun naira, ba tare da an yagalgala su ba.

Rangadin wayar da kan, wanda aka ƙaddamar a Abuja, ya samu wakilci daga Daraktan Hadahadar Kuɗaɗe, Dakta Sikiru Adetona, wanda ya ƙara da cewa wulaƙanta naira ta hanyar shafa mata datti, duƙunƙune ta ko kekketa ta da yagalgala ta yayin hadahadar kuɗaɗe yana rage mata martaba da karsashin daraja.

Ya ce: “Idan ba mu tashi tsaye mun kawar da wannan matsalar ba, to masu wulaƙanta takardun kuɗi za su ci gaba da haddasa tsadar buga sababbin kuɗin da za a maye gurbin waɗanda aka lalata da su.”

Bello ya ce darajar naira ta wuce matsayin takardar kuɗin da ake biyan ciniki ko hadahada da ita.

Ya ce naira abin alfahari ce ga Nijeriya, tauraruwar da ke haskaka ƙasar nan.

A cewar sa, “Amma abin takaici sai ka riƙa ganin wasu ba su riƙe ta da daraja, suna duƙunƙune ta, su kekketa ta, wasu su riƙa liƙi suna watsa naira a wuraren bukukuwa, wasu su riƙa rubutu kan ta, wasu ma su shafa mata datti, su yagalgala ta, ko su cumuimuye ta.”

Ya ce ƙoƙarin da ake yi don kare darajar Naira ba a kan wuyan CBN kaɗai ya rataya ba, har da ɗaukacin ‘yan Nijeriya baki ɗaya duk nauyin ya rataya a wuyan su.

Ya ce a wannan ƙoƙarin cusa wa jama’a kare ƙimar naira da daina wulaƙanta ta, akwai buƙatar haɗin-gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe, ciki har da bankunan kasuwanci, ƙananan bankunan hada-hada, ƙungiyoyin sufuri, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa, shugabannin kasuwanni, ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafafen yaɗa labarai.

Ya yi kira ga masu kasuwanci da ‘yan tireda da masu motocin haya da su taimaka wajen daina wulaƙanta kuɗi, kuma ƙungiyoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai su ma su yayata wannan kamfe ya isa gida-gida, yayin da sauran dukkan ‘yan Nijeriya tilas su zama dakarun kare daraja da ƙimar naira.

“Ta haka ne za a samu nasarar canja ɗabi’ar mutane su riƙa riƙe takardun kuɗi da daraja,” inji shi.

Yayin da bukukuwan Kirsimeti da ƙarshen shekara ke gabatowa, Bello ya gargaɗin cewa kada a riƙa ɓoye kuɗi ana kimshe su, domin yin hakan na hana wasu samun isassun kuɗaɗen da za su riƙa hada-hada, kuma yana kawo cikas da naƙasun ƙarancin kuɗaɗen da ke hannun jama’a.”

Ya bayyana cewa wannan shirin rangadin wayar da kai don hana jama’a wulaƙanta takardun kuɗaɗe, zai karaɗe jihohin ƙasar nan da ƙananan hukumomi, har ma da wasu yankunan karkara.

Shi kuwa Adetona a nasa jawabin, ya tabbatar da cewa CBN zai samar da wadatattun kuɗaɗen hada-hada a lokacin Kirsimeti da hutun ƙarshen shekara. Sai dai ya yi kira da a ci gaba da riƙe su da daraja.

Ita ma Daraktar Hulɗa da Jama’a ta CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce duk da yake haƙƙin CBN ne ya samar da takardun naira, kuma ya tabbatar wadatattun kuɗaɗe masu tsafta, to kuma ta ce haƙƙi ne mai nauyi kan kowane ɗan Nijeriya ya riƙa darajta naira, ta hanyar daina wulaƙanta ta, ya tsaftace ta kuma ya daina yagalgala ta.

Ta ce takardun naira masu tsafta sun fi kwarjini a ido da ƙima yayin hadahada.

Tags: Babban Bankin NijeriyaCBNNairaOlayemi Cardoso
Previous Post

Nijeriya tana kan hanyar kaiwa ga ƙarfin arziki mai ɗorewa, inji Tinubu

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!