• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Idris ya yaba wa Bago kan ayyukan raya Neja, ya jinjina wa aikin hanyar tarayya na ₦1.5tn

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
October 9, 2026
in Siyasa
A A
0
Idris ya yaba wa Bago kan ayyukan raya Neja, ya jinjina wa aikin hanyar tarayya na ₦1.5tn
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da membobin Ƙungiyar Tattaunawa kan Cigaban Jihar Neja (NSDF) lokacin da suka kai ziyarar ban-girma ga gwamnan, yau a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, kan zuba jari a harkokin noma da gine-ginen ababen more rayuwa, tare da bayyana aikin sake ginawa da faɗaɗa babbar hanyar tarayya ta Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora, wanda kuɗin sa ya kai naira tiriliyan 1.5, a matsayin babban ci gaba da zai bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Idris ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja, lokacin da ya jagoranci membobin Ƙungiyar Tattaunawa kan Cigaban Jihar Neja (NSDF) wajen kai ziyarar ban-girma ga gwamnan.

Ya bayyana Neja a matsayin jiha mai muhimmanci ga cigaban Nijeriya, bisa la’akari da damar da take da ita a fannin noma, matsayin ta na musamman da kuma gudunmawar da take bayarwa ga samar da wutar lantarki ta tashoshin samar da wutar lantarki na Kainji, Jebba da Shiroro.

Ministan ya yaba da yadda gwamnatin Bago ta mayar da hankali kan noma ta amfani da injina, noma na kasuwanci, bunƙasa masana’antun sarrafa amfanin gona da kuma sabunta birane. Ya ace waɗannan zuba jari na kafa tubalin sauya fasalin jihar.

Idris yana gabatar da jawabi a taron

Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da aikin sake ginawa da faɗaɗa babbar hanyar tarayya ta Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora, inda aka tsara gudanar da bikin aza harsashin aikin a ranar 13 ga Oktoba, 2026, a Bida.

Idris ya ce aikin zai inganta hanyoyin shiga al’ummomin manoma, haɗa kasuwanni da cibiyoyin masana’antu, tare da sauƙaƙa jigilar amfanin gona da sauran kayayyaki.

Ya ce: “Wannan wani gagarumin aiki ne a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri na noma da kasuwanci a Nijeriya.”

Gwamna Bago ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa jihar ta hanyar ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa na tarayya, tallafin kuɗaɗen raya ƙasa da kuma naɗa ’yan jihar a muƙaman hukumomin tarayya.

Ya ce aikin hanyar zai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, bunƙasa noma da kuma inganta harkokin kasuwanci a faɗin jihar.

Idris ya kuma jajanta wa Gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ibtila’o’i da ƙalubalen tsaro na baya-bayan nan, tare da amincewa da ƙoƙarin da gwamnatocin tarayya da jiha da hukumomin tsaro suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Tags: Jihar NejaMohammed IdrisMohammed Umaru Bagoziyaraƙungiya
Previous Post

2027: Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sa a Kaduna

Next Post

Matan Nijeriya sun ƙudiri aniyar tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027, inji Uwargida Remi a taron Arewa ta Tsakiya

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Matan Nijeriya sun ƙudiri aniyar tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027, inji Uwargida Remi a taron Arewa ta Tsakiya

Matan Nijeriya sun ƙudiri aniyar tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027, inji Uwargida Remi a taron Arewa ta Tsakiya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!