• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya ƙara wa Abdulaziz girma a aiki

Fati Abdul by Fati Abdul
June 17, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya ƙara wa Abdulaziz girma a aiki
Abdulaziz Abdulaziz yana musabaha da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro

Abdulaziz Abdulaziz yana musabaha da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara wa Malam Abdulaziz Abdulaziz girma a matsayin sa, inda ya ɗaga shi zuwa muƙamin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a (Senior Special Assistant on Media and Public Enlightenment).

Malam Abdul’aziz ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sa na soshiyal midiya, inda ya ce ya karɓi takardar tabbatar da sabon naɗin nasa a ranar Laraba.

Ya ce sabon matsayin sa ya yi daidai da tsarin ayyukan da Shugaban Ƙasa ya amince da su tun ranar 23 ga Afrilu, 2026.

Ya bayyana wannan ƙarin girma a aiki a matsayin wata babbar karramawa da kuma nuna amincewa da gudunmawar da yake bayarwa a guruf ɗin masu aikin sadarwa ta Fadar Shugaban Ƙasa da kuma a fannin yaɗa labarai gaba ɗaya.

A cewar sa, sabon matsayin ba wai karramawa ce kawai ba, har ila yau ya ɗora masa sabon nauyi da ƙalubale da ke buƙatar ƙarin jajircewa, ƙwazo da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan sa domin cimma manufofin gwamnati da kuma yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.

Malam Abdul’aziz ya miƙa godiyar sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da nuna masa amincewa da goyon baya. Haka kuma, ya gode wa shugabannin sa da abokan aikin sa a fannin sadarwa bisa haɗin kai, jagoranci da kuma hangen nesa da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan su.

Ya kuma nuna matuƙar godiyar sa ga abokan aiki, abokan sa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, yana mai cewa gudunmawar da suka bayar ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da ya samu a rayuwar sa ta aiki.

Sabon naɗin dai yana daga cikin sauye-sauyen da Shugaba Tinubu yake yi a ɓangaren sadarwa da yaɗa manufofin gwamnatin sa ga jama’a.

Tags: Abdulaziz AbdulazizmuƙamiShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da manhajar FreeTV a tsarin DSO

Next Post

Minista na so kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin kare zaman lafiya

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Minista na so kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin kare zaman lafiya

Minista na so kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin kare zaman lafiya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!