Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga suka kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, da kuma ƙauyen Kahir da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
Shugaban ya bayyana waɗannan hare-hare, waɗanda suka haɗa da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baƙi ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban ƙalubale ga haɗin kan Najeriya.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa ba za a zura ido waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin su sha da daɗi ba.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa kan fannin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Talata, Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalumai kuma matsorata.
Ya ce: “Duk wanda zai fake da duhun dare ya kashe mutanen da ba su da kariya kamar yadda aka yi a Jos da ƙauyen Kahir, to matsoraci ne marar tausayi. Manufar waɗannan maharan ita ce su haifar da ramuwar gayya domin jini ya ci gaba da kwarara,” inji Shugaban.
Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umurnin su ƙara ƙaimi wajen kamo waɗanda suka aikata laifin da kuma waɗanda ke yaɗa labaran ƙarya da nufin ruruta wutar rikici.
Haka kuma ya ja kunnen wasu ɓangarorin kafafen yaɗa labarai da ke ƙoƙarin danganta hare-haren da batun addini.
Manyan matakan da Shugaban ya ɗauka sun haɗa da:
* Kiran Jami’an Tsaro: Ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa amfani da bayanan sirri don daƙile hare-hare kafin su auku.
* Ceton Waɗanda Aka Sace: Ya ba da umurnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kahir.
* Kayan Aiki: Ya bayyana cewa gwamnati tana kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.
Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa ƙoƙarin su na shawo kan lamarin da kuma tallafa wa ayyukan ceto.
Daga ƙarshe, ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan su, sannan ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, yana mai kira ga al’umma da su ba jami’an tsaro haɗin kai don tabbatar da zaman lafiya.







