• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Mahaifiyar Nasir El-Rufa’i ta rasu

Fati Abdul by Fati Abdul
March 27, 2026
in Labarai
A A
0
Mahaifiyar Nasir El-Rufa’i ta rasu
Hajiya Umma El-Rufa’i ta dafa kan Malam Nasir El-Rufa'i tana yi masa addu'a

Hajiya Umma El-Rufa’i ta dafa kan Malam Nasir El-Rufa'i tana yi masa addu'a

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, ya shiga cikin jimami sakamakon rasuwar mahaifiyar sa, Hajiya Umma El-Rufa’i, a wani lamari da ya zo daidai da lokacin da yake fuskantar shari’a.

Marigayiyar ta rasu ne da yammacin yau Juma’a, ko da yake har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda rasuwar ta faru ba a lokacin da ake tattara wannan rahoto.

Wata majiya ta ce ta rasu ne a Alƙahira, ƙasar Masar, inda take jinyar doguwar rashin lafiya.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

Jikan ta, Bello El-Rufa’i, shi ne ya tabbatar da labarin rasuwar, inda ya bayyana hakan cikin wani saƙo mai cike da alhini da ya wallafa a soshiyal midiya.

“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Daga Allah SWT muka fito, kuma gare Shi za mu koma,” in ji shi.

“Ina sanar da al’umma rasuwar kakata, Hajiya Umma El-Rufa’i, wadda ta rasu ‘yan sa’o’i da suka gabata.

“Ita ce mahaifiyar mahaifin mu, Mallam Nasir El-Rufa’i. Muna godiya da rayuwar da ta yi, kuma muna roƙon Allah SWT Ya jiƙan ta da rahama. A madadin iyalan mu, muna roƙon addu’o’in ku.”

El-Rufai yana tura mahaifiyar sa kan kujerar gajiyayyu a Madina

Rasuwar ta zo a wani lokaci mai wahala ga tsohon gwamnan, wanda a halin yanzu yake fuskantar tuhuma daga Hukumar ICPC (Mai Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaka).

Kwanan nan an gurfanar da El-Rufa’i a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda goma da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma wanke kuɗaɗe, bayan ya shafe kusan wata guda a tsare.

Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Hajiya Umma tare da ɗan ta Malam Nasir da jikan ta

A zaman kotu na ƙarshe, Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kaduna ta dage sauraron buƙatar belin sa zuwa ranar 31 ga Maris.

Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Rilwanu Aikawa, ne ya sanya ranar bayan sauraron hujjojin ɓangaren masu gabatar da ƙara da kuma na masu kare kai.

Hajiya Umma tana sanya wa Malam Nasir El-Rufa’i albarka
Tags: El-RufaiHajiya Ummarasuwa
Previous Post

Dalla-Dalla: Abubuwan da Suka Kamata a Sani Dangane da Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna na 2026

Next Post

Hotuna: Babban taron APC na 2026

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Hotuna: Babban taron APC na 2026

Hotuna: Babban taron APC na 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!