• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙungiyoyi Suna Buƙatar Bayanai Daga ‘Yan Sanda Kan Harin Da Aka Kai Wa Gidan Sarkin Kano

NEW CITIZEN HAUSA by NEW CITIZEN HAUSA
July 8, 2025
in Labarai
A A
0
Ƙungiyoyi Suna Buƙatar Bayanai Daga ‘Yan Sanda Kan Harin Da Aka Kai Wa Gidan Sarkin Kano
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

A CIKIN sa’o’i 24 bayan harin da aka kai fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da ke Gidan Rumfa, Ƙofar Kudu, a cikin birnin Kano, wasu ƙungiyoyin farar hula da ke ƙarƙashin jagorancin One Kano Agenda, sun buƙaci a hukumomin tsaro, musamman ‘yan sanda, da su fitar da bayani kan shiru da suka yi game da lamarin.

An ruwaito cewa wata tawagar tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ce ta kai harin a daren Lahadi, a yayin da take dawowa daga gidan marigayi attajirin Kano, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, bayan kai gaisuwar ta’aziyya.

Bayanan da ƙungiyoyin suka tattara dai sun yi nuni da cewar tsohon sarkin ya bar hanyarsa ta yau da kullum da ke kai shi Mandawari, ya karkata ta Kabara wadda ke gaban fadar Gidan Rumfa, wanda hakan ya janyo harin da wasu da ake zargin na cikin ‘yan rakiyar sa ne suka kai.

Ƙungiyoyin farar hular da suka haɗa kai ƙarƙashin jagorancin One Kano Agenda, sun bayyana shiru da jam’ian tsaro suka yi a matsayin abu mai tayar da hankali wanda ke nuna gazawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar, kuma yana iya haifar da ruɗani da fitina.

Sun ce hakan na iya zama wani yunƙuri na daban don Kawo Rashin Zaman Lafiya da gangan a Jihar Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Ƙungiyoyin sun kuma bayyana Rahoton Abubuwan Da Aka Lalata da Wanda Aka Sata Kamar Haka :

Motocin ‘Yan Sanda:

Hilux ta ‘yan sanda (NPF 182D) – Mopol 9.

Hilux ta ‘yan sanda (NPF 195D) – Mopol 52.

Abubuwan da aka lalata:

Babur na Abdullahi Shehu (Jami’in ‘yan sanda)

Babur na Ibrahim Isa (Mashal din tsaro a masarautar)

Babbar ƙofa ta ƙarfe ta masarautar ta lalace matuƙa.

Wurin tsaron ‘yan sanda da ke fadar Shima an lalata shi.

Kayan Tsaro da Aka Sata:

Cikakken kayan ‘yan sanda na kamfale.

Takalman tsaro na ‘yan sanda guda ɗaya.

Majigin harsashi ɗaya – wanda ke da matuƙar hatsari.

Mutanen da suka jikkata:

Maigoma Ɗan’agundi (yana kwance a Asibitin Murtala Muhammed).

Yunusa Babba (Mashal ɗin tsaro).

Murtala Muhammed (Jami’in ‘yan sanda na musamman).

Abin da muke buƙata:

1. A gaggauta fara bincike kan harin da aka kai, Sannan a yi nazari akan abin da aka lalata kamar dukiyoyin gwamnati da kuma kai hari ga jami’an tsaro da fararen hula.

2. A gano, a kama, sannan a gurfanar da duk masu hannu akan kai wannan hari.

3. A nemo kayan ‘yan sanda da aka sata, musamman majigin harsashi wanda ke da babbar barazana ga tsaro.

4. A ƙara tsaurara tsaro a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ma gidansa baki ɗaya.

Muna kira ga hukumomin tsaro a Kano da su ɗauki matakin gaggawa da na kwarjini don kare doka da oda, da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Doka ba za ta amince da aikata laifi ba, kuma babu wanda ya fi doka, ko da kuwa yana da matsayin mulki ko iko.

Waɗanda suka rattaba hannu:

Mustapha Abdullahi – Kano Digital Media Rangers.

Comrade Salisu Gambo – Youth Mobilization By Media.

Alhaji Suleiman Idris – Northern Youth Assembly.

Malam Abdulƙadir Abubakar – One Voice Development Initiative.

Aisha Muhammad Shettima – Beyond Border Alliance.

Barr. Badamasi Gandu – Kano First Forum.

Amb. Abbas Abdullahi – Shugaban One Kano Agenda.

Barr. Mukhtar Musa – Sakataren One Kano Agenda.

Tags: 'yansandahariSarkin Kano Muhammadu Sanusi IIɓatagariƙungiyoyi
Previous Post

Shekara Ɗaya Bayan Komawa Kan Karagar Mulki: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

Next Post

Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris

Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba - Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!