Mashawarcin Gwamnan Kano kan Harkokin Addini, Sheikh Usamatu Salga, ya yi kira ga Hukumar Shari’a ta jihar da ta ruɓanya jajircewar da take yi wajen bayar da horo ta hanyar shirya wa ma’aikata taruka.
Salga ya bayyana hakan a wajen taron ƙara wa sakatarorin Hukumar Shari’a na ƙananan hukumomin Kano 44 sanin makamar aiki, akan ayyukan su.
Taron dai na kwanaki biyu ne, wato Asabar da Lahadi, kuma yanzu haka yana gudana a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Gwamnatin Kano ce dai ta shirya taron na ƙara wa juna sanin, a ƙarƙashin ofishin Hukumar Shari’a ta Jihar Kano da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Sheikh Abbas Abubakar Daneji.
Sheikh Usamatu Salga ya kuma buƙaci dukkanin jami’an gwamnatin Kano da su riƙa bai wa Hukumar Shari’a ta jihar haɗin kan da ya kamata ta yadda za su ƙara samun dama wajen gudanar da ayyukan su cikin nasara.
Da yake nasa jawabin a yayin taron, Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce an shirya taron ƙara wa juna sanin ne bisa yadda suka lura da raunin sakatarorin hukumar na ƙananan hukumomin Kano 44, wajen gudanar da aiki.
Ya ce don haka ne aka shirya musu bitar don ƙara musu sani ta yadda za su riƙa gudanar da aikin su yadda ya kamata.
Tunda farko, da yake jawabin maraba a yayin taron, Kwamishina na Biyu a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan”Abba, ya buƙaci waɗannan sakatarori da dukkanin shugabannin hukumar na ƙananan hukumomin jihar 44, da su ƙara haɗa kan su tare da kawar da dukkanin abin da zai iya kawo bambanci.
Dakta Bala Muhammad, malami a Sashen Koyar da aikin Jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, ya gabatar da maƙala a yayin taron a kan muhimmancin riƙe sirrin gwamnati da ofis da kuma amfanin yin hakan ko akasin haka, har ma ya shawarci dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu riƙe sirrin wurin da suke aiki, don guje wa fuskantar matsala.
Taron ya samu halartar al’umma da dama, kuma ciki har da Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano Sheikh Ahmad Tijjani Auwal da Kwamishina na Ɗaya a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Gwani Hadi Ɗahiru Yakasai. Sai daraktocin hukumar da sakatarori da ma wasu shugabannin hukumar na ƙananan hukumomin Kano da sauran su.





