Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin samar wa manoma rancen kuɗi ba tare da ruwa ba, domin rage musu nauyin kuɗaɗen gudanar da noma, ƙara yawan amfanin gona da kuma sauƙaƙa farashin abinci ga ’yan Nijeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne a wajen gangamin zaɓen APC a Inugu, inda ya kuma yi alƙawarin inganta samar da wutar lantarki, bunƙasa ababen more rayuwa da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatin sa na ƙoƙarin samar da yanayin da zai taimaka wa manoma su samu kuɗin gudanar da noma cikin sauƙi, domin ƙara samar da abinci da rage tsadar rayuwa.
Ya kuma buƙaci al’ummar Inugu da su fito su zaɓi APC a dukkan matakan zaɓe na gaba, yana mai cewa goyon bayan jam’iyyar zai taimaka wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.






