• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Minista ya dakatar da ƙarin kuɗin sayen lasisin gidajen rediyo da talbijin

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 9, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Minista ya dakatar da ƙarin kuɗin sayen lasisin gidajen rediyo da talbijin
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da shugabannin Ƙungiyar Masu Gidan Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (BON), lokacin da suka kai masa ziyara yau a Abuja 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da shugabannin Ƙungiyar Masu Gidan Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (BON), lokacin da suka kai masa ziyara yau a Abuja 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, tare da shugabannin Ƙungiyar Masu Gidan Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (BON), lokacin da suka kai masa ziyara yau a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya dakatar da duk wani ƙari na kuɗaɗen sayen lasisin kafa gidajen rediyo da talbijin har sai baba-ta-gani, a wani yunƙuri na magance matsalolin da ke addabar masana’antar.

Hakan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da masu gidajen suke yi kan ƙarin kuɗaɗen gudanar da harkokin su.

Idris ya bayyana matakin ne a ranar Litinin a Abuja, lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Ƙungiyar Masu Gidan Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (BON), ƙarƙashin jagorancin shugaban ta, Senior High Chief Tony Akiotu.

Ministan ya ce dakatarwar tana daga cikin matakan da ake ɗauka domin shawo kan ƙalubalen da masana’antar yaɗa labarai take fuskanta a Nijeriya, tare da samar da yanayin da zai ba ta damar bunƙasa da ɗorewa.

Ya ce: “An dakatar da duk wani ƙarin kuɗin lasisi. Haka kuma an dakatar da duk wani nazarin da ta shafi kuɗin sayen lasisi har sai baba-ta-gani. Ina umurtar hukumar NBC da ta tabbatar da bin wannan umurni yayin da muke nazarin halin da ake ciki.”

Idris ya kuma umurci Darakta-Janar na Hukumar Gidajen Rediyo da Talbijin (NBC) ɗin da ya gaggauta nazarin Kundin Ƙa’idojin Gudanar da Ayyukan Yaɗa Labarai na Ƙasa domin tabbatar da cewa dokokin da ke jagorantar masana’antar sun dace da sauye-sauye da sababbin abubuwan da ke faruwa a cikin ta.

Dangane da sauya tsarin yaɗa shirye-shirye zuwa na zamani (DSO), ministan ya yi alƙawarin shirya taron masu ruwa da tsaki domin tattauna batutuwan da ba a warware ba.

Ya kuma bayyana cewa ya riga ya umurci Hukumar Kula da Talla ta Nijeriya (ARCON) da ta tabbatar da cikakken aiwatar da tsarin biyan kuɗin tallace-tallace cikin kwanaki 45, sakamakon buƙatar BON na ganin an tabbatar da bin wannan ƙa’ida.

Haka kuma, ya tabbatar wa da tawagar cewa ma’aikatar sa za ta tattauna da masu ruwa da tsaki kan matsalolin samun kuɗaɗen gudanar da harkoki cikin sauƙi da kuma rabon mitocin yaɗa shirye-shirye.

Idris ya jaddada muhimmiyar rawar da gidajen rediyo da talbijin suke takawa wajen ƙarfafa mulkin dimokiraɗiyya, tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma bai wa ’yan ƙasa damar samun sahihan bayanai.

Ya buƙaci masu gudanar da gidajen rediyo da talbijin da su kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa, adalci da ɗabi’un aikin jarida, musamman yayin da ƙasar ke shirin babban zaɓen 2027.

Ya kuma buƙaci masu gudanar da gidajen rediyo da talbijin da su tabbatar da cewa rahotannin da suke bayarwa sahihai ne kuma suna taimakawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

Tun da farko, Cif Akiotu ya yaba wa Idris bisa rawar da ya taka wajen shawo kan matsaloli yayin ƙaddamar da shirin DSO a watan Yuni na 2026.

Ya ce taron masu ruwa da tsaki da ministan ya shirya ya taimaka wajen magance damuwar da ake da ita kan tabbatar da adalci da daidaito tsakanin masu gudanar da gidajen yaɗa labarai.

Ya lissafa bitar Kundin Ƙa’idojin Gudanar da Ayyukan Yaɗa Labarai na Ƙasa, kuɗaɗen lasisi, hauhawar kuɗaɗen gudanar da harkoki, samun kuɗaɗen gudanar da harkoki, rabon mitocin yaɗa shirye-shirye da aiwatar da tsarin biyan kuɗin tallace-tallace cikin kwanaki 45 a matsayin wasu daga cikin manyan ƙalubalen da masana’antar ke fuskanta.

Akiotu ya ce ƙungiyar su ta BON tana ganin tattaunawa, shawarwari da sasanci su ne hanyoyin da suka dace wajen kauce wa rikice-rikicen da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da kyakkyawar alaƙa a masana’antar.

Ya kuma nemi ministan da ya ci gaba da taimaka wa ƙungiyar wajen shawo kan ƙalubalen da mambobin ta suke fuskanta.

Idris ya taya BON murnar nasarar gudanar da babban taron ta na 82 a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, tare da sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a masana’antar domin ƙarfafa ta da tabbatar da ɗorewar cigaban ta.

Tags: BONgidajen rediyo da talbijinlasisiMohammed Idrisziyara
Previous Post

Tinubu zai ƙaddamar da hanyar jirgin ƙasa ta Kaduna zuwa Kano ran 3 ga Disamba

Next Post

Kotu ta umurci a ƙwace kadarorin Abubakar Malami 48 masu darajar Naira biliyan 212

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Kotu ta tsare Malami, matar sa da ɗan sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Kotu ta umurci a ƙwace kadarorin Abubakar Malami 48 masu darajar Naira biliyan 212

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!