Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Jidda na ƙasar Saudiyya yau Laraba bayan kammala aikin Umrah a birnin Makkah.
Jirgin shugaban ya tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jidda da misalin ƙarfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya, zuwa Abuja.
Mataimakin Gwamnan Yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud, tare da Jakaden Nijeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da Babban Jami’in Ofishin Jakadancin Nijeriya a Jidda, Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya, su ne suka raka shugaban zuwa filin jirgi.
Kafin tashin sa, Tinubu ya gana da Mataimakin Gwamnan Makkah a taƙaice a fadar baƙi ta masarauta da ke filin jirgin.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne shugaban ya jagoranci tawagar Nijeriya wajen gudanar da Umrah, ciki har da ɗawafin Ka’aba.
Haka kuma, a ranar Lahadi an ba Tinubu damar shiga cikin ɗakin Ka’aba, inda shi da wasu daga cikin tawagar sa suka yi sallah raka’a biyu.
A yayin da yake cikin Ka’aba, shugaban ƙasar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya azurta Nijeriya da zaman lafiya mai ɗorewa, tsaro, haɗin kai da wadata. Ya kuma roƙi Allah ya ba shi shiriya, hikima da ƙarfin gwiwar ci gaba da yi wa al’ummar Nijeriya hidima.
Haka nan, ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Nijeriya da shugabannin ta da al’ummar ta albarka, tare da fatan cewa bambancin da ke tsakanin al’ummar ƙasar zai zama tushen ƙarfi, haɗin kan ƙasa da wadata da kowa zai amfana da ita.
Gwamnati ta ce ziyarar shugaban zuwa Saudiyya ta ba shi damar yin tunani a kan al’amuran rayuwa, tare da gode wa Allah da yin addu’o’in neman zaman lafiya da cigaban Nijeriya, tare da sabunta ƙudirin sa na gina ƙasa mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata.
Tinubu ya kuma nuna godiya ta musamman ga Mai Kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman, bisa karamci da kyakkyawar tarbar da suka yi masa da tawagar sa, musamman damar shiga cikin Ka’aba domin gudanar da addu’o’i.
Shugaban ya bar Saudiyya da sabunta imani, godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, da kuma ƙudirin ci gaba da aiwatar da shirin Renewed Hope Agenda, domin gina Nijeriya mafi inganci ga dukkan ’yan ƙasar ta.
Daga cikin tawagar shugaban akwai mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu, da gwamnonin jihohin Sakkwato, Jigawa, Kaduna, Borno da Yobe, da sauran manyan jami’an gwamnati.







