• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala

ALI KANO by ALI KANO
October 26, 2026
in Tsaro
A A
0
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Umar Ibrahim Gandi Maradun, mai shekaru 22, tare da matasan Izala suna gudanar da atisayen fareti a ƙarƙashin jagorancin wasu manya a bidiyon

Umar Ibrahim Gandi Maradun, mai shekaru 22, tare da matasan Izala suna gudanar da atisayen fareti a ƙarƙashin jagorancin wasu manya a bidiyon

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Nijeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa kuma mai zaman kan sa kan wani bidiyo da ya yaɗu a soshiyal midiya, wanda ya nuna yara da matasa suna gudanar da atisayen fareti a ƙarƙashin jagorancin wasu manya sanye da kayan sojoji masu alaƙa da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a wa Ikamatus-Sunnah (JIBWIS).

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana damuwar ta kan bidiyon, wanda ake zargin ya nuna matasan suna rera taken neman a ba su bindigogin AK-47 domin kai hare-hare kan waɗanda suka kira kafirai a Inugu da Jos a ranar Lahadi.

Amnesty International ta bayyana taken a matsayin wani mummunan misali na yadda ake amfani da yara wajen cusa musu aƙidun tashin hankali da ƙiyayya, tana mai gargaɗin cewa irin waɗannan ayyuka na iya ƙara rura wutar ƙiyayya tsakanin addinai da kuma ƙarfafa tashin hankali.

Ƙungiyar ta buƙaci hukumomi da su gudanar da bincike kan waɗanda suka shirya atisayen, su gano asalin bidiyon da wurin da aka ɗauke shi, tare da nazarin taken da aka rera da kuma manhajar koyarwar da ake amfani da ita a irin waɗannan shirye-shiryen matasa.

Haka kuma, Amnesty ta yi kira da a ɗauki matakan da suka dace domin kare yaran da abin ya shafa, ciki har da samar musu da tallafin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da ilimi, domin kare su daga tsattsauran ra’ayi.

Ta kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wani mutum ko ƙungiyar addini da aka samu da laifin amfani da yara wajen yaɗa rashin haƙuri ga mabambantan ra’ayoyi ko tauye ‘yancin addini.

Ƙungiyar ta jaddada cewa kare yara daga kalaman ƙiyayya, atisayen da ke kwaikwayon horon soja da kuma cusa musu tsattsauran akidu wajibi ne da ya rataya a wuyan gwamnati bisa dokokin ƙasa da na ƙasa da ƙasa.

Ta yi nuni da Dokar Kare Haƙƙin Yara (Child Rights Act) da kuma yarjejeniyoyin haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa, ciki har da Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Haƙƙin Yara, a matsayin dokoki da suka tanadi kare yara daga tashin hankali, kalaman ƙiyayya da kuma ɗaukar su ko horar da su a ayyukan da suka yi kama da na rundunonin soja.

A cewar Amnesty, amfani da shirye-shiryen matasa ko ƙungiyoyin koyar da addini wajen cusa musu akidun gaba da ƙiyayya yana barazana ga tsaron jama’a tare da raunana ‘yancin addini.

Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su ɗauki matakin gaggawa domin gano gaskiyar abin da ya faru dangane da bidiyon, tare da tabbatar da cewa an kare yara daga ayyukan da za su iya jefa su cikin tashin hankali da rashin haƙuri ga mabambantan ra’ayoyi.

Tags: addiniAmnesty International NigeriabidiyoIzalakisatsaro
Previous Post

Taron Kaduna: Arewa ta Bayyana Matsayar Ta Kan Tinubu

Next Post

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!