• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Idris na so ‘yan jaridar intanet su tantance sahihancin labari kafin su wallafa shi

* Masu rubutun intanet na Jihar Neja sun yi alƙawarin gudanar da aikin jarida mai nagarta da kare muradun ƙasa

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
October 12, 2026
in Labarai
A A
0
Idris na so ‘yan jaridar intanet su tantance sahihancin labari kafin su wallafa shi
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Abuja, wanda Ƙungiyar Masu Rubutun Intanet, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Samar da Abubuwan Yaɗa Labarai ta Jihar Neja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Abuja, wanda Ƙungiyar Masu Rubutun Intanet, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Samar da Abubuwan Yaɗa Labarai ta Jihar Neja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu rubutun intanet da sauran ma’aikatan kafafen yaɗa labarai na zamani a Nijeriya da su tabbatar da sahihancin labari kafin su wallafa ko yaɗa shi, musamman ganin yadda shafukan sada zumunta suka sa kusan kowane mai wayar salula ta zamani zai iya zama ɗan jarida, edita kuma mawallafin labarai.

Idris ya yi wannan kiran ne a wani taron kwana ɗaya da aka gudanar a Abuja, wanda Ƙungiyar Masu Rubutun Intanet, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Samar da Abubuwan Yaɗa Labarai ta Jihar Neja (Niger Bloggers, Online Publishers and Content Developers Group) ta shirya, a ƙarƙashin taken: “Nijeriya Farko, Kafin Komai.”

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ɗin ne ya karɓi baƙuncin taron, wanda Yahaya Mohammed Usman da Nurudeen Isiyaku Daza suka kira.

A jawabin sa, ministan ya jaddada buƙatar tsare gaskiya, ƙwarewa da la’akari da muradun ƙasa wajen yanke shawarwari na edita, yana mai cewa tsarin kafafen yaɗa labarai na gargajiya yana da hanyoyin tantance labarai da ke tabbatar da sahihancin bayanan da ake wallafawa.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su goyi bayan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai wajen cigaban ƙasa.

Idris ya yi alƙawarin ci gaba da yin tarurruka a kowace kwata ta shekara tare da masu rubutun intanet, mawallafa labarai a intanet da masu samar da abubuwan yaɗa labarai na Jihar Neja, tare da alƙawarin mayar da tarurrukan na gaba na kwana biyu domin samar da ƙarin damar bunƙasa ƙwarewa, musayar ilimi da halartar mutane da yawa.

Tun da farko, babban baƙo mai gabatar da jawabi a taron, Dakta Yunusa Umar, wanda ƙwararre ne a harkokin ƙasashen waje da nazarin yankuna daga Jami’ar Nazarin Harsunan Waje ta Beijing da ke ƙasar Chaina, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji yaɗa munanan labarai game da ƙasar su saboda fushi ko takaici.

Umar ya jaddada muhimmancin kishin ƙasa da sadarwa mai nagarta, yana mai gargaɗin cewa labaran ƙarya ko na kushe Nijeriya suna iya ɓata mata suna a idon duniya.

Yayin da yake bayar da labarin abin da ya same shi shi kan sa, ya bayyana cewa an taɓa hana shi biza ta zuwa wata ƙasa, wanda ya danganta da munanan labarai game da Nijeriya da ke yawo a soshiyal midiya a lokacin.

Ya kuma kwatanta ‘yancin faɗin albarkacin baki da ake da shi a Nijeriya da takunkumin da aka ƙaƙaba wa wasu ƙasashe, ciki har da Chaina, yana mai cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su yi amfani da haƙƙin su cikin nagarta tare da yin la’akari da illolin kalaman da suke yi a bainar jama’a.

A saƙon fatan alheri da ya gabatar, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya yi kira ga ma’aikatan yaɗa labarai da su kiyaye gaskiya, adalci, ƙwarewa da ɗa’ar aikin jarida.

Abdulaziz ya amince da haƙƙin ‘yan ƙasa na kundin tsarin mulki na sukar manufofin gwamnati da jami’an ta, to amma ya jaddada cewa ya kamata irin wannan suka ta kasance mai ma’ana, mai tushe da tsare gaskiya, kuma ta dace da muradun ƙasa.

A ƙarshen taron, masu rubutun intanet, mawallafa labarai a intanet da masu samar da abubuwan yaɗa labarai daga Jihar Neja ɗin sun sha alwashin za su inganta aikin jarida mai nagarta, bayar da rahoto bisa gaskiya da kare muradun Nijeriya, tare da amfani da haƙƙin su na kundin tsarin mulki na tuhumar jami’an gwamnati.

Bugu da ƙari, mahalartan sun amince da ƙudirori da suka ɗaura ɗamarar kiyaye mafi girman matsayin aikin jarida, ɗa’a da mu’amala mai nagarta da jama’a.

Sun kuma sake jaddada alƙawarin su na nuna Nijeriya ta hanya mai kyau tare da tuhumar jami’an gwamnati ta hanyar bayar da rahoto bisa gaskiya da suka mai ma’ana.

Mahalarta taron sun gode wa Idris saboda ɗaukar nauyin taron da kuma ci gaba da tarurruka da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai na zamani na Jihar Neja.

Sun kuma yaba wa Abdulaziz saboda gudunmawar da ya bayar a tattaunawar kan aikin jarida mai nagarta da cigaban ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma yi alƙawarin amfani da ilimin da ta samu a wajen taron domin inganta kishin ƙasa, bunƙasa ƙwarewar aiki da amfani da kafafen yaɗa labarai na zamani cikin nagarta.

Tags: 'yan jaridaintanetMohammed IdrisNejasoshiyal midiya
Previous Post

Tinubu ya naɗa Yusuf Bichi muƙamin shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata

Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!